Total Pageviews

Wednesday, November 29, 2017

ANFANIN ILMI AIKI DASHI

AMFANIN ILIMI AIKI DA SHI
--------------- --------------- --------------- --------------- --------------- --------------- --------------- --------------- ------ Mallam Ibn Kayyum yace: Abubuwa
goma basu da amfani,
Na daya ilmin da baa aiki dashi,
Na biyu aikin da ba ayishi saboda
Allah ba, kuma baa kan sunnar
Annabi saw ba, .
Na uku dukiyar da ba a ciyar da ita ba,
mai ita bai amfana da ita a duniya ba
kuma baiyi aikin lahira da itaba,
.
Na hudu da zuciyar da babu kaunar Allah a cikin ta da shaukin haduwa
dashi da nutsuwa dashi.
Na biyar da gangar jikin da baa
sarrafashi wajen biyayya ga Allah ba
da yiwa addinin sa hidma,
Na shida da soyayyar da bata ginu ba, akan neman yardar wanda ake so, da
yi masa biyayya ba.
Na bakwai da lokacin da akayi
hasararsa wajen rashin amfani dashi
domin gyara abinda akayi sakacin
yinsa a baya ko aikata biyayya da nagarta.
.
Na takwas da tunani cikin abinda
bashi da amfani
Na tara da yin hidma ga mutumin da yi
masa hidma, ba zata kusantaka ga Allah ba, ko amfanin duniya
.
Na goma da nuna kwadayinka ko
tsoranka ga wanda shima ragamar sa
tana wajen Allah, sai yadda yayi dashi,
bashi da ikon tunkudewa kansa cuta ko jawowa kansa amfani ko mutuwa
ko rayuwa ko tashi bayan mutuwa.
.
Allah kasa muyi kyawawan aiki, da
kyawawan karshe, da kyakkyawan
sakamako...,

Sunday, November 26, 2017

ILLOLIN DAKE CIKIN WASU SAFIN SADARWAR ZAMANI

Hausawa kan ce ana za ton wuta a makera sai a same ta a masaka, wannan magana ta yi daidai da yadda akan yi zaton cewa wasu shafukan internet na kumshe ne da tarin illoli da cututtukan da ka iya lalata ta wasu kuma basu da shi amma abin ba haka yake ba Hakika akwai wasu kebantattun shafukan Internet da suka fi ko’ina hatsarin shiga sabo da irin abubuwan da ake boyewa a cikin su,
wadanda idan mutum ya ziyarci irin wadannan cututtuka zai iya sanyawa na’urarshi cututtukan da zasu iya lalata na’urar da kuma hanyayoyin da za su kiyaye ko su tsare a lokacin da suka fada cikin irin wadannan shafuka. Mun kasa wadannan shafuka kusan gida biyar (5) wanda za mu sanya alama wacce idan muka sa kafin muyi bayanin wannan wuri yake nuna cewar illa ko rashin illar shiga wannan shafi. Zai iya yuwuwa bayanai da zamu fadi a wannan Mujallar Duniyar Computer ya zamanto an sami canji sakamakon irin ci gaba da ake yi da kuma gyare gyaren da wasu shafuka ko kuma gidajen internet suke yi a lokacin da suka fahimci cewar akwai matsaloli tare da shafukan su. Da fatar za a karanta da idon ba sira kuma a kiyaye, domin manufarmu shine a zama babu wata matsala a computer mu. irin hotuna da zaka iya gani na ‘yan matan turawa ko na motoci ko na mawaka na iya zama ba hotu bane da aka sasu domin kallo kawai, za su iya yuwuwa akwai cutarwa da ke nade a jikinsu. Haka nan mafi yawan amsoshin da mutum kan bincika a shafi na google na iya zama amsa ga mai bincike, zai kuma iya yuwa su zama ciwon kai ga computer ka. Jin dadin kallon wasu video da kake yi a internet ko kuma sauko da su (Downloading) jin dadin da annashuwar na iya komawa bacin rai da damuwa a na’urarka. Na san sau tari mutum yana jin ana gaya mishi hatsarin da ke cikin shafukan internet, wannan haka yake, wasu shafukan suna da hatsari, wadansu kuma za ka shiga ciki kayi wadakarka, babu abinda zai same ka. Zaka iya daukan ko wane irin mataki domin ka tsare na’urarka, zai yi wahala ya zama kai mai son shiga kowane irin shafi a internet a ce baka kwaso ko da malware ba, ko
kuma a kwace ragamar tafiyar da akwatin e mail din ka, a rinka turo maka da sakonni na banza da wofi, ko kuma a kwace maka sirrin da kake ajiye wa a na’urarka, ya zama bayanan ka, bayanan katin kudin ka,
da dai wadansu bayanai wanda baka son kowa ya sani. Irin wadannan dalilai sune suke sa mutum ya dauki matakin neman tsare kanshi daga fadawa hannun ‘yan baranda wadanda burinsu shine su ga sun lalata ko sun kwace ragamar na’urarka ta hanyar virus da
malware da dai sauransu. Kuma yana
da kyau mutum yasan irin cutar da zai iya samu a lokacin da ya shiga wani shafi, da kuma abinda zai yi domin ya samu tsari kada wani abu a cutar da shi. Cutar shafukan da ake samu a internet ba iri daya ba ne, godiya ga Allah, Mujallar Duniyar Computer ta yi kokarin bincike kuma ta karkasa su irin wadannan shafuka har gida biyar kamar yadda na fara bayani a farko. Saboda haka matakin farko shine kada ka shiga shafin da baka amince da shi ba, domin yin haka zai iya kawo maka matsala. Ka yi amfani da bayanan da zamu yi maka a matsayin
hanyar shiriya. Cuta ta 1: Flash files da ake zargin suna hade da abinda zai lalata na’urarka. Inda ake samunsu: Mafi yawancin shafukan da suke amfani da Flash : Abobe sune kamfanin da suke yin wannan program na yin Flash wanda
wadansu suke yin amfani da shi su daura wadansu umarni (Codes) na malware da idan mutum ya ziyarci shafin da suke na’urarshi ta kamu da cuta. Wani karin cutarwa dangane da su flash website shine wadanda suke
kirkiran shafukan kuma su goya musu wadannan malware suna amfani da shi flash din ne sabo da shi flash ana rubuta wani tsari da zai tafiyar da shi, sai su yi amfani da wannan damar su daura musu umarnin da idan ya shigo na’urar ka zai basu wata kafa da zasu yi maka barna. Wani abin haushi sukan yi amfani da tsarin irin na Cookies, shi kuwa Cookies ya tunatar da browser (program da ake yin amfani da shi wajen bude shafukan internet) shafukan da mutum ya ziyarta da ita, sannan kuma koda ka share Cookies din browser ka, to na flash baya fita, yakan bar baya da kura Ina son mutane kada hankalinsu ya tashi suce ke nan duk wani shafi da muka gani da flash ya na da malware ko virus ke nan. Amsar ita ce a a, domin mafi yawan shafukan da zaka shiga na kasannan kusa kadanne wanda basu da flash a kansu, kuma bana tsammanin akwai wani wanda yake iya yin wannan program da zai cutar a wannan lokaci. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Domin ka tsare kanka daga farmaki irin na flash program, ya kamata ko da wani lokaci ka rinka amfani da gyararran plug-in na flash kuma ya kasance shi plug-in din yana tafiya tare zamani. (Plug-in shine wasu canje-canje da kamfanonin da suke yin software su ke yi a kai a kai domin cire wasu matsaloli da mutane suke fuskanta tare da program din su). Sannan zaka iya shirya tsarin yadda kake son idan flash ya sauko daga internet ya zai yi yayi aiki a cikin
na’urarka. Cuta ta 2: Kutsattsarin Links wadanda zasu iya kai ka ga shafukan da zasu iya cutarwa Inda ake samunsu: Twitter : Macuta a harkar yadda kwayoyin cutar da na’ura (Scammers) lallai suna son Twitter sabo da shi shafin dandali da raja’ane ga kananan Link, sannan kuma a Twitter mutum zai iya rage tsawon Link zuwa dan gajere. Da wannan dalili ne, Scammers suke amfani da dandalin Twitter domin boye Link da yake kai mutum zuwa mugun shafi wanda ziyarar shafin na da hatsari. Abu ne mai sauki mutum ya boye malware ko kuma cuta a irin wadannan gajerun links. Kuma kusan dukkan irin wadannan gajerun link a karshe suna kai mutum zuwa ga shafin da zaka sami (Trojan horse). Yadda abin yake ka kalli saman browser ka zaka ga inda aka rubuta misali kamar haka (http://www.duniyarcomputer.com),
a in da ka ga wannan shi ake kira address to zai iya yuwuwa a cikin shafin internet ka ga an rubuta cewar idan kayi clicking nan misali salisu za ka shiga shafin cin gasa, wato duk inda ka ga rubutu a shafin internet a cikin shafin kuma da layi a kasan shi, shi a ke kira link, to yadda su macutan suke yi maimakon idan kaga wannan link idan ka kai dan yatsan mouse zai iya nuna maka wurin da zaka shiga, to tsarin da Twitter suka yi shine maimakon ka ga misali http:// www.duniyarcomputer.com sai kawai kaga http://~QseHH kawai. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Abu mafi sauki shine idan kaga wannan link din kada ga latsa shi. Na san kuwa abin zai baka dariya domin
an hanaka yawo a twitter kenan? Wata hanyar da zaka bi kuma itace kayi amfani da kananan application da ake attaching din su da Twitter wanda su suna taimakawa wajen biyyana asali sannan cikakkiyar hanyar da wannan link zai kai ka. Amma shawara mafi inganci idan har ba ka san waye ya aiko maka da link ba, kuma baka san inda wannan link zai kai ka ba, abu mafi dacewa shine ka rabu da shi. Cuta ta 3: Sakon email da ga macuta ko kuma attachment da zai kai ga inda za’a kwashe maka mahimman bayanai ko kuma ka dibo Virus Inda ake samunsu: Akwatin Email din ka : dangane da abinda ya shafi emil da yadda ake amfani da shi wajen aiko da sakonnin na banza, wadanda su wadannan sakonni manufar turosu shine idan ka bude su, sai su aiko maka da kwayoyin cutar da computer. Ko da yake kamfanonin da suke harkar bayar da Email ko kuma ake amfani da su suna kokari matuka wajen warware sakonnin da suka yi kama da na cutarwa. Mafi yawan sako da ake turowa daga wasu kamfanoni wanda suka kumshi talla da sayar da haja, su scammers suna amfani da adireshi ko kuma sunan wani kaya sannan sai su goya wannan Virus ko kuma Malware a jikin shi sakon, yadda idan kaga, a misali “Saura kwana uku mu rufe bayar da Visa ta Amurka kyauta” da kaga irin wadannan talla sannan daman kai mai bukatar Visa ne sai kawai ka bude wannan sako, ka danna wannan sako ke da wuya sai kawai abinda suke so ya faru a na’urarka sai kawai ya faru. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Kada ka yarda da ko wani irin sakon da baka san waye ya aiko maka ba, ko kuma ba kayi magana da su zasu aiko maka ba. Idan har kaga irin wannan sako kuma kana bukatar ka fahimci ina aka sa gaba, to, sai ka ki latsa wannan Link, ka shiga website da ka ji cewar suke da alhakin wannan sako idan sakon sabo da kai ne, to, kaga babu matsala. Cuta ta 4: Malware da ake boye su a jikin Video ko Music ko kuma Software wajen Downloading Inda ake samunsu: Shafukan Torrent : Shafukan Torrent da gidajensu na Internet basu da doka wajen tafiyar da sana’arsu, tun da daman kusan dukkan kayan da ke cikin irin wadannan gidaje na sata ne, kuma babu wata doka ko order a lokacin da wanda ya dibo kayan wasu yana son ya ba wasu kyauta akan cewar dole wannan kayan su zama masu tsabta. Wannan dalili yasa scammers suka fi amfani da gidaje irin na Torrent wajen yada Virus da Malware. Ben Edelman wanda yake sashin bincike sannan kuma Farfesa ne a Harvard Business School yace “Ina ganin babu wani shafi a Internet wanda ya fi ko ina hatsarin shiga irin gidajen Torrent, domin su basu da doka akan abinda ake zuba musu, domin ba a sayar da kaya a ciki. Shi yasa nake ganin shafukan da suke nuna tsiraici zasu fi shafukan Torrent tsabta, idan ka dangantasu da cewar ana biyan su kudi domin amfani da kayansu”. In ji Ben Edelman. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Hanya mafi dacewa ita ce, kada ka shiga wannan shafi, sannan kuma ka
guji irin wadannan kayayyakin da basu da garanti wajen amincin wadanda suka bayar da su. Amma idan har ka dage akan cewar dole sai
ka shiga, to, kayi amfani da wata na’urar da ka san babu mahimman bayanan ka a cikin ta. Kuma ya kasance idan zaka saukar da kaya daga irin wadannan shafuka ka rinka kokarin karanta jawaban da mutane suke yi a kasan shafin, idan kayan da kake son kayi downloading akwai matsala zaka ji idan akwai wani matsala, idan kuma babu matsala zaka ji shima. Idan kuma dai ka nace sai ka dauko shi, kuma babu wanda yayi bayanin lafiyarshi? To, idan ka saukar sai ka jira sai bayan kamar kwana biyu, sai ka bude shi. Amma shima da sharadi ya zamanto kana amfani da Anti- Virus mai lasisi kuma ya zama koda wanne lokaci kana Updating na anti- virus din. Cuta ta 5: Malware a cikin Hotuna ko Video wanda akwai tsiraici a cikin shi. Inda ake samunsu: Amintattun Gidajen nuna tsiraici : Shafukan da ake nuna majigi na tsiraici suna da matsalar tsaro ba kamar sauran shafuka da ake kallon majigi ba kai tsaye, amma hakan ba yana nuna maka an kai karshen bayanin ba ke nan. “Babu tantama shiga cikin irin wadannan shafukan zubar da mutunci ba yana nuna maka cewar yana da cikakken hatsariba, amma idan sana’arka kenan wata rana zaka tsinci kanka a wajen da zaka sami cuta” in ji Roger Thomson babban mai bincike a ma’aikatar AVG (wanda su suke yin AVG Anti-Virus) ya kara da cewa “Wannan abun bantakaici ne, tunda ko ka tsare kan ka daga shiga irin wadannan shafuka, ba yana tabbatar maka da ka tsaru ba ne. Domin mafi yawan gidajen Internet Scammers sukan yi fasa kaurinsu su saka irin wadannan abubuwa na cutarwa”. Kamar yadda na fadi a baya, amintattun shafukan nuna tsiraici, yana da matukar wahala su bari a saka Malware a ciki, domin suna son koda wani lokaci abokanen huldansu su ci gaba da hulda da su. Amma yana da wahala ka iya raba tsakanin amintattun shafukan batsa da malware. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Kayi hankali da irin Video da zaka sauko da shi, kuma ka kiyaye dukkan wani Video da zai ce sai ya dauko Codecs sannan ka iya amfani da shi, ko kuma kayi amfani da toolbar irin na Norton ko McAfee da SiteAdvisor da ke Firefox domin idan akwai gidan da zaka shiga akwai matsala su fada maka. Wani mataki na biyu shine idan har kace zaka shiga wannan shafi, to ka yi amfani da wani computer domin tsaron mutuncin ka da na iyalanka. Cuta ta 6 Trojan Horses wanda ake wufintar da mutum a matsayin video codecs, daga karshe malware su shiga computer ka. Inda ake samunsu: Websites da ake saukar da Video, ko kuma a peer-to-peer networks. : nasan babu tantama idan ka taba kallon video kai tsaye daga internet nasan an taba ce maka ka saukar da wani codecs da zai baka damar ka kalli wannan video. Codes wani dan karamin application ne da yake taimakawa wajen a iya kallon video a
internet. Maganar gaskiya sau tari irin
wadannan codecs din basu da matsala misali kamar DivX codec. Amma fa ka sani wadansu website din suna saka video a da za a kalla a internet kai tsaye sannan su makala mishi wannan codecs wanda akwai malware a jikin shi da kuma zarar ka saukar da shi ko kuma ka kalleshi sai
computer dinka ta samu matsala. Matakin da za ka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Mataki mai kyau shine ka tabbatar dukkan wani abu da zaka kalla kai tsaye a internet idan yace kana bukatar codecs wajen kallon shi kasan su wane ne masu video din, kamar misalin video’n da ake samu a dandalin YouTube.com da kuma Vimeo idan kaga sun ce kana bukatar codecs zaka iya saukar da su domin su amintattun gidajen ne, haka nan kamar gidajen ka amince da su cewar ba zasu saka tsiya a cikin website dinsu ba, ko kuma site da ka san ka biya kudi ne ka ke kallon abinda suka saka. Amma kuma idan kai ma’abocin kallo ne, ko
da wane lokaci kana son kallon wasanni ko kuma labarin ko kuma irin shirye-shiryen wasan kwaikwayo irin daga gidajen Hulu.com ko TV.com ko kuma ABC.com da kuma iTunes.com to suma suna da aminci domin sunfi peer-to-peer network . Cuta ta 7 Taswira a jikin wayarka wacce take baka damar ganin wurare daga jikin ta. Inda ake samunsu: a wannan wayarka mai tsada (Smartphones) : kasuwar wayoyin hannu da ake kira Smartphones har yanzu jaririyace, haka yake ita ma hanyar cutarwar irin wadannan wayoyi shima bai shaharaba, idan ma akwai abin da ya kamata mu saka idano akai shine taswira da take iya nuna mana wurare da muke son gani da kuma bayanai, domin nasan akwai mugayen mutane da suke kan hanyar cutarwa sannan kuma suna nan suna kara wanzuwa. Abu na farko da aka samu shine akwai wani game da ake sakawa a waya mai tsarin Android wanda a karshe aka gane cewar shi wannan game yana matsayin dan leken asiri a wayarka. Haka akwai wani website mai suna pleaserobme.com wanda yake nuna cewar ai wane kaza baya gida wanda haka hatsari ne ga tsaron shi. Dangane da irin wannan misalan, tabbas akwai application da suke da amfani a cikin smartphone kamar wanda zai iya gaya maka wajen da ka nufa, ko kuma ka sauka a wani gari da baka sanshi ba zai iya fada maka wajen da kake da kamar misalign hotel ko kuma dakin abinci dake kusa da kai. Ko da yake kamfanin Apple masu yin irin su IPhones kwanakin baya suka kara kaimi wajen ganin sun kiyaye mutuncin masu amfani da kayansu, tun daga abinda ya shafi bayanan sirrin su, sunayensu da wurin da yake da dai makamantansu. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Mataki mai kyau shine ka kiyaye da dukkan wani sabon abu da baka sanshi ba, ko kuma ka lura da kyau da irin hotunan da suke bayyana a fuskar smartphone dinka, sannan kuma ya kasance ba ko wane irin application zaka gani ba kamar daga facebook.com ko kumaFourSquare wanda suke nuna maka wurare a yarda da shi ba, sannan kuma ya kasance kana da cikakkiyar masaniyar inda zaka shiga. Cuta ta 8 Gidajen yin bincike (search engine) wanda suke da guba, wanda a karshe su kai ka zuwa ga website dake da malware. Inda ake samunsu: Search Engine (Gidajen da ikin su shine kawai bincike) : Guba da Search Engine suke kai mutum ya samu asali ne daga irin shafun da mugaye suke kirkira su saka saka wani abu da suka san ya shahara ko kuma mutane suna yawan bincike a kanshi, sai su goya shafin malware sannan kuma su saka dukkanin wani tsari da suka san cewa Search Engine website suna nema wajen cika sharadi wanda daga baya idan ka binciki kamar wane kayane yafi kyau ta bangaren kaza, ko kuma wannen babban labara ko kuma a baka kaya goda goma wadanda suka fi daraja sai kawai ka fada tarkon su. Kamar yadda kamfanin da suke yin Anti-Virus mai suna McAfee suka fada bayan sun gudanar da wani bincike, suka ce kashi 19% na sakamako da mutane suke yin bincike a Search Engine kamar irin su shahararrun ‘yan wasan fim na turai kamar Cameron Diaz ko kuma irin screensaver da mutane suke bincike suna kai mutane ne zuwa ga gidajen website masu malware. Haka kuma suka ce irin su Facebook da labarai da dumi-duminsu suma wurin kai hari ne ga irin wadannan mutane. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Idan har baka san gidan da zaka shiga ban a internet, sannan kuma ka shiga search Engine website kayi bincike, to, ka natsu da kyau ka karanta URL (tsanin da zaka hau yakai ka gidan da kake son shiga) ka tabbatar shine inda kake so ka shiga. Kada kawai ka rufe idanun ka duk abinda ka ga sakamakon shi ya fito maka ka kawai ka latsa URL ka shiga. Cuta ta 9 Takardu masu PDF da ake iya wawuntar da kai har ya saka maka malware. Inda ake samunsu: wurare guda biyu (2) akwatin email naka, da kuma website da aka yi hacking dinshi. : a lokacin da Hackers suka ga kamfanin Microsoft ma kara kaimi wajen ganin sun rage yawan malware da virus da ake jifan Windows dashi sai, sai Hackers suka canza sababbin hanyoyi da kuma salo da zasu yi amfani da shi wajen watsa irin wadannan cututtuka a computer. Daya daga cikin matakan da suke dauka suma Hackers din shine ta amfani da takardun PDF, wanda suke iya lullube malware a jikin shi su saka shi. Ana kiran irin wadannan PDF da (poisoned PDF) wato PDF mai guba. Kuma inda suke kutsa irin wadannan file masu guba shine cikin akwatin email dinka kaga sako da baka san waye ya aiko da shi ba da attachment. Ko kuma suyi kokari su kwace ragamar wani gidan
internet su watsa irin wadannan takardu. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Babban mataki shine ka tabbatar koda wane lokaci kana amfani da sabon Adobe Reader (kyauta ne ba a sayar da shi), haka kuma zaka iya amfani da wasu Program da suke iya bude PDF wanda ba kamfani Adobe suka yi ba, kamar yin amfani da sabon Foxit Reader. Yin amfani da sabon PDF reader zai kasance ya zaman maka garkuwa akan dukkan wata kafa da Hackers suke iya amfani da ita wajen su cutar maka da computer ka. Za kuma ka iya hana Adobe Reader taka ta bude dukkanin wani attachment da ban a PDF, ta shiga Preferences sannan ka click Trust Manager sannan ka cire Allow opening of non-PDF file attachments with external application. Illa iyaka. Ko da yake sabon Adobe Reader 10.0 da ake da shi idan shine a jikin computer ka ka sami tsaro. Cuta ta 10 Mugayen video da ake hadasu da lalatattun abin kallo (player) domin a kwace ragamar computer ka. Inda ake samunsu: Website da ake saukar da Video : Gwanayen fasakwaurin gidajen internet suna yin amfani da codecs da video kamar yadda suke yin amfani da shi a cikin PDF idan suka saka surkulensu kai kuma ka shiga kaga video’n ka dauko ka kalla sai na’urarka ta fara maka dangerda. Suna yin amfani da abun amfani da dama wadanda mutane suka fi shahara wajen yin kallon video da su a cikin computer, amma a wanda yafi ko wannen shahara shine a Quick Time Player, wacce ake amfani da ita wajen kallon video da ya kare da .mp4. Matakin da zaka dauka idan ka ziyarci wannan shafi Babu wani mataki da zaka dauka wajen kare kanka da irin wadannan video matukar kai mai son kallon video ne a internet ko kuma sauko da su ill aka rika ko da wane lokaci updating players dinka, domin wadannan kamfanoni masu yi player suna kara matakai na tsarewa da kuma gyaran wani matsala da zasu iya fuskanta a kowane lokaci. Idan kuwa kana da sha’awar kallo to ka kasance kana kallo a gidajen da yake suna da aminci kamar YouTube da kuma kayi amfani da gidan kallo irin na iTunes. Cuta ta 11 Shafukan Intanet waɗanda suke
tilasta wa mai shigan su saukar da
Malware lokacin da ya ziyarce su. Inda ake samunsu: Shafukan da Hackers su kwace ragamar
sa. A Turance ana kiran irin waɗannan
shafuka da ’Drive-by Download ’ shafuka ne waɗanda suke tilasta wa
wanda ya ziyarce su domin ya
saukar da waɗandu program zuwa
ga Kwamfutarshi ba tare da ya sani
ba. Za kuma a iya samun irin
waɗannan matsalar a shafuka da dama. Kodayake mafi yawancin
shafuka da ake ?ir?iransu domin
saukar da irin waɗannan ?ananan
program sau tari da gangan suke yin
haka, waɗansu kuma rashin sa’a ake
yi har hackers su ?wace ragamar tafiyar da ha?ar shafin, sai su saka
abin da suke bu?ata ba tare da su
kan su masu asalin shafin sun sani
ba. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci wannan shafi Abu na farko shi ne idan ka san kai
mai yawan shiga kowane irin shafi
ne to, yana da kyau ya kasance koda
wane lokaci Kwamfutarka ta na da
cikakken tsaro, kuma kana updating
din shi, kuma kana scanning Kwamfutar domin bincikar ko irin
waɗannan program su shigo cikin ita
Kwamfutar. Domin mafi yawan Anti-
Virus suna iya gano irin waɗannan ?
ananan program kuma su na iya cire
su kai tsaye. Cuta ta 12 Anti-Virus Software na ?arya ko bogi
waɗanda aka yi su domin a ?arar
maka da kuɗinka ko kuma a kwashi
bayanan sirrinka. Inda ake samunsu: Cikin akwatin Imel ɗinka da
shafuka da aka yi Hacking
ɗinsu. Sau tari mutane bas u cika mai da
hankalinsu a kan abin da ya shafi
anti-virus software ɗinsu ba. Domin
kuwa shi anti-virus ya fi zama komai
hatsari a cikin harkokin da mutum
yake yi tare da Computer. Irin waɗannan Anti-Virus na bogi mutum
na iya saka su a cikin Kwamfutarsa
bayan ya samo su a internet ya yi
downloading ɗinsu da nufin cewar
zai duba lafiyar Kwamfutarsa. To, a
daidai lokacin da ya gama saukowa ka saka shi a cikin Kwamfutar sai
bayan ka umarce shi da ya duba
lafiyar Kwamfutar zai faɗa ma ka
cewar ya samo matsaloli ma su yawa,
waɗanda dole ka ce ya cire su.
Saboda haka, da zarar ya cire kamar ashirin cikin ɗari biyu sai ya ce shi na
gwaji ne, idan ka na bu?atar a cire
dukkanin virus da ya kamo to sai ka
sayi cikakken shi. Saboda haka da
zarar ka ɗauko credit card ɗinka ka
saka domin ka siya sai kawai su saci bayanan wannan kati ko dai su
kwashe dukkannin abin da shi katin
ya ?unsa na kuɗ ko kuma su ri?a
sayan kaya ma su tsada da katin. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafin Duk lokacin da ka tsinkayi wani
sabon sa?o da ya fita yana sanar da
kai cewar wani sabon Virus ya shigo
cikin Kwamfutarka kuma ka tabbatar
cewar ba Anti-Virus din da ka saka
ba ne ya fito da wannan sa?on to nan take ka kashe Kwamfutar, ka
tashe ta ta SAFE MODE sannan ka kunna anti-virus ɗinka ka umarce shi
da ya binciki ita Kwamfutar domin ya
gani idan da gaske ne akwai ba?on
virus. Kodayake ba kowane Anti-virus ba
ne ya ke da ilimin kowane virus ba,
shi ya sa yana da kyau mutum ya
sayi antivirus na ?warai sannan ya ri?
a yin updating ɗin shi a kowane
lokaci. Idan kuma haka ta faskara bayan ka kashe ita Kwamfutar ka
tashe ta a SAFE MODE amma daga
baya ka fahimci cewar yanayin
yadda Kwamfutar ta ke yin aiki ya
chanze, to sai ka nemo ?wararru
domin su gano maka matsalar. Cuta ta 13 Talla a shafuka da suke kai mutum
zuwa ga masu cuta ko saukar da
malware a Kwamfuta Inda ake samunsu: Kusan kowane irin shafi da ya ke
ɗauke da talla a cikin shi. Ba kowane irin shafi ba ne da za ka ga talla a cikinsa ne ya ke ɗauke da
talla da zai kai ka zuwa ga irin
waɗdancan mugayen shafuka ba.
Kusan ita talla da ake ganinta a
shafukan internet su ake amfani da
su wajen biyan wahalhalun shi website ɗin. Su irin waɗannan
tallukan da ake ganinsu a shafuka
ma su aikin cuta ko kuma fasa ?
wauri a internet sukan ?ir?iri irin tasu
talla wanda ya yi kama da talla ta
zahiri, wanda idan mutum ya latsa domin ya ga abin da wannan tallar
ta ?unsa sai kawai ya faɗa tarkon su. A shekarun baya, kamfanin jaridar
nan na ?asar Amurka ’New York
Times’ a cikin shafinsu na internet
cikin rashin sani su ka saka talla na
shafin scammer wanda ya kawo ma
su hallartar shafinsu su ka faɗa hannun ’yan baranda. Haka su ma
kamfanin Google sun taɓa saka talla
daga irin waɗannan gidaje cikin
rashin sani wanda ya kai ga al’umma
faɗawa ciki. Kamar yadda wani babban ma’aikaci
a kamfanin GFI Software Eric Howes
ya faɗa ne cewa “masu fasa ?wauri a
internet kullum sake samo hanyoyin
cuta suke yi, yanzu burin su shi ne su
ga sun lalata dukkanin wa ta kafa wacce ake talla da ita, ta hanyar kai
mutane zuwa ga shafuka da suke
ɗauke da ?wayoyin cutar da
Computer ta yadda wanda ya ziyarci
shafukan zai sami illa ga na’urarsa. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafi Idan mutum ya faɗa irin waɗannan
shafuka waɗanda akwai talla a cikin
su, mutum ya lura da kyau ya
tabbatar da cewar ya san shafin da
zai shiga, sannan kuma ya sani
cewar ba dukkanin talla ba ne ke ɗauke da irin waɗannan cutuka ba.
Kuma yana da kyau mutum ya
kasance ana’urarsa akwai anti-virus
mai lasisi. Cuta ta 14 Application da suke facebook masu
yin tambayoyi. Inda ake samunsu: Facebook Application da ake samu a Facebook
mafi yawancinsu ba suna zuwa ba ne
da matsala, sai dai mutane da dama
suna ganin cewar Hackers a wannan
lokacin suna yin amfani da irin
wannan application waɗanda ake yin amfani da su wajen yin
tambayoyi domin amsawa. Irin
waɗannan application suna iya bijiro
maka a shafinka na facebook tare da
hoton da kuma sunan abokinka da
cewar yana tambaya game da matsayin abu kaza, ko kuma ’Shin ka
yarda cewar wane zai iya yaudarar
ka?’ Irin waɗanna tambayoyi da
makamantansu, wasu hackers su
suke shirya shi ’application’ din
domin su ɗauki bayanan sirri na mutum su yi amfani da shi daga baya
domin cimma burinsu. Kodayake irin
waɗannan application din kafin su
fara aiki a cikin shafinka na sada
zumunci na facebook sai ka ba su
izini, shi ya sa yana da kyau matu?a ko da wane lokaci ka ri?a bibiyar
wajen saita shi shafin facebook ka na
duba waɗanne application suke
amfani a cikin shafinka, sannan
kuma su na da amfani a wurinka ko
ba su da amfani. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafin Ya zamanto koda wane lokaci ka na
mai tantance wane irin application ne
z aka yi amfani da shi a shafinka na
facebook, sannan kuma ya zamanto
ka na yawaita bibiyar bayanai na shi
wannan application. Ka kasance kana bibiyar wajen saita facebook
naka, ka na kuma domin wane
abubuwa ne ya kamata mutane su
gani tare da kai ko kuma kada su
gani tare da kai. Cuta ta 15 Shafukan intanet waɗanda za su
matsa maka da cewar ka yi ’Sign Up’
daga baya su sayar da adireshin ka
na imel zuwa ga spammers. Inda ake samunsu: Shafuka waɗanda ake kira da ’Free
Electronics’ Babu shakka akwai irin waɗannan
shafukan waɗanda ake iya gane ta
hanyar yadda suke tunkarar masu
mu’amala da su ta hanyar tallata
masu wata haja, kamar misali ka ga
’Get a free iPad’ ko kuma ’Get a free notebook! Gaskiyar magana irin
waɗannan shafukan a zahiri ba su da
wata matsala, domin abu ne mai
matu?ar wahala idan ka shiga irin
waɗannan shafuka ka sami malware
ya shigo cikin Kwamfutarka. Amma matsalar shi ne bayanan ka da ka
shigar lokacin da ka yi ’sign up’ za a
iya sayar da su ga waɗansu ’yan
kasuwa. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafi Idan ka tsinci kanka a irin waɗannan
shafuka yana da kyau kafin ka
shigar da bayanan ka ka karanta
sharuɗansu da ?a’idojin yin amfani
da shafinsu ’privacy policy’ wanda a
cikinshi idan ka karanta za su iya ga ya maka cewar ga abin da za su yi da
bayanan da su ka karɓa a wurinka.
Shi ya sa yana da kyau duk wanda
zai shiga wani shafi da ake bukatar
ya cike ’form’ to ya tabbatar ya
karanta dokoki da ?a’idojin shiga shafukansu domin ya san me zai faru
da bayanan da ya shigar a nan gaba.
Kodayake wani lokaci a kan samu
bayanai na ?arya a wurin ma su
shafuka amma dai irin waɗannan bai
ciki shahara ba. Amma dai ko ma me su ka faɗa ko su ka rubuta babu
wani abu da ke iya tabbatar da
cewar za su sayar da bayanan ka ko
ba za su sayar ba. Cuta ta 16 Shafukan sada zumunta ’Social
Network’ waɗanda za su zambace ka
har ka saukar da malware a cikin
kwamfutarka daga baya ya aikawa
da macuta bayan ka. Inda ake samunsu: Shafukan sada zumunci ’social
networks’ Ban da application mai yin tambayoyi da kuma ?ananan links da
suke kai mutum ga shafukan da za
su cutar da Kwamfutarsa. Shafukan
sada zumunci kamar Facebook ya
yi ?aurin suna da kuma samun
magauta wajen ?o?arin yaɗa dukkanin wani abu da zai iya zama
barazana ga shafukan sada
zumuncin. misalin Scammers za su
iya ?wace ragamar tafiyar da shafin
sada zumuncin ka na facebook
sannan su saka wani ɗan ?aramin link da zai ba abokananka damar
shiga wannan shafi wanda in da za a
kai su shi ne wajen cutar da
Kwamfutarsu. Wannan kuwa ya haɗa
da ?wace ragamar tafiyar da shi
shafin daga hannun mai shi da yin amfani da dukkanin ma su hulɗa da
shi da ɗiban bayanan sa da kuma kai
shi hannun masu fasa ?wauri a
intanet. Babbar matsalar da ma su amfani da
shafukan sada zumunci irin su
facebook da twitter za su fuskanta
shi ne barazanar malware, da
adware da kuma spyware ta suke
yawo sa?o-sa?o na internet. Mutane za su iya ganin abubuwa ma su ban
sha’awa wanda suka haɗa da
hotuna da kuma video wanda a
zahiri manufar saka irin waɗannan
hotuna domin ka faɗa hannun ’yan
baranda ne. Wani lokaci ma za ka ga application da zai gyara maka
shafinka na facebook ko twitter
’widget’ wanda kai ma da kan ka z
aka yi sha’awa amma bayan ka saka
su a cikin shafinka sai ka samu babu
abin da zai kai ka illa ya kawo maka su adware da malware ko kuma
spyware a cikin Kwamfutarka ko
kuma shafinka na sada zumunci. Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafin Kada ka yarda da kowane irin link da
ka gan shi a shafin sada zumunta na
facebook ko twitter, ko da kuma
ɗaya daga cikin abokanan ka ne ya
saka shi. Kafi ka latsa wannan shafi
ya fara shiga asalin shafin da aka ce wannan maganar take ka duba ka
gani da gaske ne ko kuma yaudare.
Ko kuma ka kira shi wannan abokin
na ka ka tambaye shi ko shi ne da
kanshi ya saka wannan link ɗin ko
kuwa ba shi ba ne. Idan kuwa kai ne aka yi amfani da
shafinka ake aikawa da mutane irin
waɗannan bayanai, sannan kuma ka
ke zargin cewar an ?wace ragamar
tafiyar da shafinka ne, to mataki na
farko shi ne ka canza ’password’ ɗinka. Ya na kuma da kyau ka ri?a
ziyartar ɓangarorin shafukan
zumunta da suke warware bayanai
na cututtuka da ke cikin su, domin
akwai shafuka da ke cikinsu
waɗanda su ne suke bayani a kan irin waɗannan miyagun mutane.
Waɗanda suke facebook za su iya
shiga ’security page’ waɗanda kuma
suke twitter za su buɗe @spam da
@safety domin sanin mene ne
matsalar tsaro da ake fuskanta a irin waɗannan shafuka na sada zumunci. Cuta ta 17 Saka bayanan barkatai da suka
shafeka a cikin shafukan sada
zumunci Inda ake samun su: Shafukan sada zumunta ’social
networks’ Mutane ba su cika damuwa da wane
irin bayanai za su saka ba a cikin
shafukan su na zumunta, za ka samu
samari da ’yan mata suna zuba
bayanai da bai dace kowa ma ya sani
ba sai dai su a cikin shafukan sada zumunci. Irin waɗannan bayanai ba
wani matsala ba ne ga lafiyar
computer ko kuma su shafukan. Sai
dai matsalar a nan ita ce bayyana
bayanai da za su iya cutar da kai kan
ka da kuma bayanai waɗanda wani ka iya amfani da shi domin ya yi abin
da bai dace ba. Kamar misali za ka samu samari da
’yan mata suka saka bayanai wanda
ya shafe su, ko kuma ya shafi
iyalansu, ko kuma ya ke faruwa cikin
gidan su, ko kuma labarin cewar
gobe ko yau zan je wuri kaza, duk irin wannan yana faruwa a cikin
facebook da twitter da 2go wanda
mutum bai san wane ne ke bibiye da
shi ba a cikin wannan shafi, sannan
kuma mene ne zai biyo baya, Matakin da za ka ɗauka idan
ka ziyarci shafin Wannan ba wani abu ba ne, domin mutum zai rage saka bayanai ne barkatar, da kuma lura da abubuwan da mutum yake yi a cikin shafukan sada zumunci.

Friday, November 24, 2017

ANDROID TANA CHIN AMANAR MUTANE

Mafi akasarin wayoyi masu amfani da manhajar Android, na daukar bayanan mutane da mika su ga kamfanin Google, koda kuwa tsarin nuna bayanan mutun a kashe yake a wayar shi.
Kamfanin jaridar Quartz, suka bayyanar da wannan rahoton, dake bayyanar da cewar duk wasu wayoyin android, na nadar bayanan mutane a yayin da suke kusa da Ariyar kamfanoni waya, da kuma aika duk bayanan ga shafin Google.
A cewar wani manazarcin hakkin bil’adam, ya bayyanar da wannan a matsayin “Cin amana” su kuwa kamfanin na Google, sun tabbatar ma gidan jaridar na Quartz da cewar, basu ajiye wadannan bayanan, kuma zasu yi gyara a na’urorin su don su daina karbar wadannan bayanan.
Matsalar dai na shafar wayoyin android ne da suke dauke da tsarin ‘Google Play’ idan yana kunne a wayar su, dama dai shi tsarin Google play, anyi shine don ya dinga daukar bayanai, musamman wadanda suka shafi manhajoji a wayoyin mutane.
An dai iya gano cewar mafi akasarin wayoyi masu amfani da manhajar android, sun kwasar bayanan mutane wadanda suka hada da inda mutun yake a kowane lokaci, daga bisani suke aikama kamfanin Google.

TARIHIN MASARAUTA DAMAGARAM

Liste des Sultans du Damagaram
(L'arbre généalogique) .
Cette liste recense les Sultans de Zinder depuis 1731 :
1731 - 1746 : Malam Younous dan Ibram, né en 1688, mort en 1746
1746 - 1757 : Baba dan Malam
1757 - 1775 : Tanimoun Babami
1775 - 1782 : Assafa dan Tanimoun, mort en 1782
1782 - 1787 : Abaza dan Tanimoun
1787 - 1790 : Mahaman dan Tanimoun "Babou Tsaba"
1790 - 1799 : Daoudou dan Tanimoun
1799 - 1812 : Amadu dan Tanimoun "Na Cihanza"
1812 - 1822 : Saleman dan Tintouma, mort en 1831
1822 - 1841 : Ibram dan Saleman (1er règne)
1841 - 1843 : Tanimoun dan Saleman "Baki Jataw", "Dari" (3e règne), né en 1811 mort en 1885
1843 - 1851 : Ibram dan Saleman (2e règne), mort en 1851
1851 - 1851 : Mahaman Kace dan Ibram, régna durant quelques mois
1851 - 1880 : Tanimoun dan Saleman "Baki Jataou," "Dari" (2e règne)
1880 - 1880 : Kiyari dan Tanimoun, régné durant quelques mois
1880 - 1885 : Tanimoun dan Saleman "Baki Jataou," "Dari" (3e règne)
1885 - 1893 : Saleman "dan Aysa" dan Tanimoun "Karami"
1893 - 1899 : Amadou dan Tanimoun "May Roumdji", "Kouran Daga". Il a résisté contre la colonisation française, le capitaine Cazemajou perit sous son coup. Il est mort en 1899
1899 - 1906 : Amadou dan Tanimoun (dan Basa)
1906 - 1921 : Ousman Bellama, régent en 27 février 1921, vacant en 27 février 1923
1923 - 1950 : Barma Moustafa
1950 - 1978 : Sanda Oumaru dan Amadou, mort en 1978
1978 - 2000 : Aboubakar Oumarou Sanda, né en 1950
2001 - 2011 : Mahamadou Moustafa (Kakali), né en 1942
Depuis le 29 juin 2011 : Aboubakar Oumarou Sanda ( 2em règne ), né en 1950.

Wednesday, November 22, 2017

YAN'UWA MUSILMAI AYI HATTARA DA MAKIRCHI KAHURAI

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!
Yan uwa masu sayen sabuwar Android phone Arika lura.
Domin yahudawa suna saka COMPLETE QURAN Aciki Amma Acikin suratu Al imran sunkara wasu kalmoni kuma karin gashi nan Abayyane. Wani babban malami dake jami ar dan
fodio sokoto mai suna malam yahaya kaura shine yaturo wannan post.
Kuma muna rokon musulmi duk wanda yakaranta ya daure yawatsa ma sauran
musulmi dan kowa ya amfana.
Ya Allah kakarya kafurci da magoya bayansa.

Tuesday, November 21, 2017

MATSALAR SAURIN SANYEWAR BATRIN WAYA

Matsalar zukewar batirin waya da
sauri, kin yin cajin batirin cikin
hanzari da makalewar manhajoji
lokacin son yin amfani da su,
kadan ne daga matsalolin da suke
addabar masu amfani da wayar Android. Amma In Sha Allahu zamu
taimaka wurin kawo manyan dalilai
da suke kawo wadannan
matsalolin da kuma hanyar
magance su. Tsayar da Manhaja Abu na farko shine sanin wadansu
manhajoji ne suke shanye batir da
wuri, sannan mene ne amfanin su a
lokacin da suke yin aiki. Domin a
wani lokaci mutum zai iya kunnan
application a wayarsa kuma bai rufe su ba sannan ya sake bude
wadansu. To barin app a kunne
suna aiki a karkashin kasa, na
daga cikin abubuwan da suke
zuke batiri da sauri. Amma domin sanin wadansu
manhajoji ne suke yin aiki a
karkashin kasa kuma ya yanayin
jan batiri da suke yi, mutum na
bukatar ya shiga settings>Battery.
Wannan zai sa kaga wadansu manhajoji ne suka fi zukar cajin
batir da kuma shin wadanda kake
son yin amfani da su, su ne ko
kuma wanda dole wayar tana da
bukatar su domin ta yi aiki ne? Idan manhajojin wayar ce ke
butakarsu to dole ka yi hakuri ka
barsu su ci gaba da aikin su, domin
hana su aiki zai kawo matsala ga
aikin da ita wayar take yi. Amma
idan manhajoji ne wadanda suke taimaka maka wurin yin aiki to sai
ka danna force stop. Akwai manhajoji masu dinbin yawa
a Play Store wadanda suke
taimakawa wurin sanin hakikanin
mai yake faruwa da batirin wayar
mutum. Mu a nan zamu iya ba da
shawarar saukar da GSAM Battery Monitor. Idan ka saukar da
wannan manhajar, zai iya daukan
kwanaki yana binciken lafiyar
batirin wayar da kuma abubuwan
da suke zukarsa. Bayan ya
kammala zai baka cikakken rahoto dangane da batirin. Canza sabon Batir Wani lokaci zaka iya samu cewa
wayar da mutum ke amfani da ita
tsohuwa ce. Misali kamar yadda da
yawa daga cikinmu suke siyan
wayar hannu wacce wani yayi
amfani da ita, ko kuma amfani da yawa da aka shigo da su daga
wasu kasashe amma kuma ba
sababbi ba. To gaskiyar magana
shi ne, idan har ka duba cewa babu
irin wadancan manhajoji masu aiki
a karkashin kasa masu zuke batir, kuma ka rage hasken fuskan
wayar, to magana ta gaskiya shi ne
ana bukatar sabon batir a wannan
wayar. Kamfanonin da suke yin batirin
waya sun ce ana iya yin cikakken
cajin waya har sau dubu daya
(1000) kafin ya fara saurin
zukewa, amma shima hakan ya
danganci wani kamfanin ne yayi batir din. Idan ka yi dace wayar ana iya cire
batir din ta, to babu matsala sai a
cire batir din a canza shi da sabo,
amma kuma idan irin wayoyin da
ba a cire batir din su ne, to yana da
kyau ka kaiwa kwararru ko ma kamayar da wayar zuwa ga
kamfanin da suka kera ta idan a
garin da kake akwai su, su cire
maka batir din su mayar da sabo. A wurin canjin batir akwai korafi da
jama’a suke yi musamman idan
suka sa sabon batir sai su ce shima
sabon baya dadewa, ko kuma
yana dadewa bai yi caji ba. To
akwai matsaloli guda biyu ga hakan. Matsala ta farko shine ba a
duba karfin batirin da wayar take
bukata ba. Domin bakin da ake
zura batir yayi daidai da naka
amma kuma karfin da wayar take
take bukata bai kai ba, matsala ce, kuma idan batir din bai kai karfin
da wayar ke bukata ba zai yi saurin
zuke batir din. Cajar Wayar bata aiki
yadda ya dace Matsala ta biyu kin yin caji da sauri,
shima yana da alaka da sabon
batirin da ka saka, misali ka saka
batirin da yake da 1000mAh kuma
sai ka sami cajar wayar da take sa
karfin 300mAh to yana nuna maka cewar sai kayi jira har sau uku
kafin ta cika. Wadannan matsalar
abin lura ce kuma haka ake
magance su. Shi yasa yake da kyau sosai duk
lokacin da mutum ya ke son sayan
caja to ya tabbatar ya sayi ta
kamfanin wayarsa. Wani lokaci
amfani da caja mai karfin da tafi na
batiri shima matsala ne, domin zai yi saurin kona sinadaran da suke
ajiyar caji da wuri, kuma gasa
batirin da sauri zai iya lalata shi ba
da jimawa ba, kuma wani lokaci
koda ka samo cajar asali da aka yi
domin wayar sai ka ga bata iya yin komai a wayar. Android System yana
amfani da batir sosai Daya daga cikin abin daya fi komai
zukar batir shi ne Android System.
Android System shine babbar
manhajar da take taimakawa
wayar domin ta yi aiki kamar yadda
ya kamata, tsayar da ita tamkar tsayar da wayar ne ko kuma lalata
ta. Ga ka’ida na wadanda suke yin OS
na Android sun ce Android System
bai kamata ya wuce kashi ashirin
da biyar cikin dari (25%) na batirin
wayar ba. To amma idan aka samu
ya wuce haka, to ya nuna cewa akwai matsala sosai, kuma babu
wata hanya da za a iya magance
wannan sai ta hanyar ragewa
wayar babbar manhajar da ita
kanta wayar take amfani da ita. Misali ace wayar tana amfani da
nadroid Lollipop ne sai ka dawo da
ita zuwa Android Kit-kat. Akwai
hanyoyi da dama da ake amfani da
su wurin ragewa OS an Android
daraja da ake samu a shafukan intanet, kawai ka rubuta
downgrade (sunan wayarka). Yin
hakan shi ne kawai mafita, amma
mu sani hakan kuma na matsayin
kayiwa wayar flashin ne, amma
wani abun jin dadi koda lokacin da kake kokarin rage mata daraja an
sami matsala zaka iya yin factory
reset, wayar zata dawo daidai. Google Play Services
yana zuke batir Google Play Services shima yana
daga cikin abubuwan da suke
zuke batir da wuri, abin haushi
shine ba zai yiwu ka tsayar da shi
ba, domin shi ke taimakawa wurin
ganin manhajojin da suke cikin wayar suna da alaka tsakaninsu da
wanin su, musamman ta wurin
musayar bayanai. Amma duk da
haka akwai yadda zaka iya rage
wannan cajin. Je
Settings>Applications>All>Google
Play Services sai ka taba maballin
Clear cache. Wannan zai goge duk
wani abubuwa da wannan
manhajar ta ke tattare da su sannan ta fara gina wadansu,
wanda wannan zai rage shan batir,
zaka iya sake yin haka kowane
wata. Kashe Auto-
Brightness Dangane da matsalar hasken
fuskar waya, kusan da yawa daga
cikin mu mun fi barin cewar wayar
mu ta rinka lura da haske da kanta
wato auto brightness. Barin wayar
ta rika lura da shi da kanta ba shi ke nuna hakan daidai bane. Matsalar a nan ita ce, censor da
yake jikin wayar yana aiki tukuru
wurin sanin wani wuri ita wayar
take, shin akwai haske mai yawa
ko kuma babu, idan akwai haske
to sai fuskar wayar yayi duhu, idan kuma akwai dubu a wurin sai ta yi
haske, saboda haka barin sa a auto
yana taimakawa wurin ganin cin
batir. Yadda idanun mu suke bukatar
haske ya sha banban da na kowa,
saboda haka yana da kyau ka
tsayar da wayar ka zuwa hasken
da ka san shi ya fi dace da kai,
kuma hakan zai taimaka wurin ganin batirin baya karewa da wuri. Rage dadewar
disashewar hasken
waya Kamar yadda muka sani hasken da
ke fita ta fuskan waya na daya
daga cikin abubuwan da suke
zuke batir musamman wayoyin
Android. Saboda haka lura da
tsawon lokacin da wayar take yi cikin haske sosai yana da amfani. Lura da tsawon lokacin yana da
matukar muhimmanci domin a
wani lokaci wasu sukan bar
hasken ya kai kusan minti biyar ko
goma kafin yawar ta disashe
haskenta ko kuma ma ta tafi barci. To kamar dai yadda na fada
dadewar hasken fuskar wayar
yanayin zukar batir. Yana da kyau mu rage daga dogon
lokaci zuwa gajere, misali daga
minti guda zuwa dakikoki ishirin
ko kasa da haka. Hakan zai
taimaka wurin kara rage cinyewar
batirin waya. Lura da ‘yan
kanzagin app
(widgets) da masu
aiki karkashin kasa Wadannan manhajoji da akek kira
da Widgets su wakilan manhajoji
ne da suke tsayawa a fuskar wayar
mutum suna sanar da shi wadansu
al’amura da asalin manhajar take yi.
Misali manhajar duba yanayi, wato Weather App, manhaja ce mai
zaman kanta amma kuma
wadanda suke yinta sai su yi mata
dan kanzagi (widgets) wanda zai
wakilci shi babban da bai bukatar
kodawane lokaci sai an budeshi za aga abin da ke ciki. To irin wadannan manhajoji
kasancewar akwai guda daya ko
biyu nasan mutum ba zai damu ba,
amma yana da kyau mu sani cewar
irin wadannan manhajoji suna aiki
ne a karkashin kasa domin aiwatar da ayyukansu. To idan mutum
yana da su da yawa a cikin
wayarsa to ya sani haka saurin
shanyewar batiri zata kara kazanta. Saboda haka, irin wadannan
manhajoji irin na labarai masu
neman shiga intanet da yin aiki ta
karkashin kasa yana da kyau. Haka
irin manhajojin da suke bukatar yin
update kodawane lokaci suma suna da matsalar cin batiri wani
lokaci yana da kyau mutum ya
tsayar yin automatic update na
waya ya sa shi zuwa wani
ayyanennen lokaci kamar sau daya
a wata. Shima hakan zai taimaka wurin rage ci batiri. Wannan shi ne dan kadan daga
wasu abubuwa wanda muka ga
suna daga cikin musabbabin
cinye karfin wutar batiri, kana
da wata matsala? Mu tattaunata
a wannan wuri!

YANDA AKE ANFANI DA RETOURS NA ANDROID APPS

Android] YADDA ZAKA GYARA BACK DA HOME DA MENU BUTTONS A WAYAR ANDROID IDAN SUKA
DAINA TA6UWA
.
Kamar yadda yawancin masu amfani da wayar android suna iya fuskantar irin wannan matsalar musamman
idan wayar taka ta android ta fado ta tsage kokuma sanso dinta ya ta6u sai kaga wannan madannun guda
uku acikinsu sun dena ta6uwa yadda ya kamata kokuma ya denayi kwata kwata,
.
kunsan ana iya samun irin wannan matsalar to idan haka ta faru ga kai ko waninka to insha Allah zaka iya
gyara wannan matsalar ba saika chanja sansor ba
.
Abin da zakayi kawai shine da farko kayi download na wani application mai suna
.
Simple Control.apk
.
Zaku iya search dinsa a google Bayan kunyi download dinsa sai kuyi instal dinsa sannan kuyi active dinsa
shikkenan kun gama zakuga ya fito daga kasan screen dinku shikkenan sai kuci gaba dayin amfani dashi
kamar yadda kukeyi da na asalin wayar.
.
Allah ya bada sa,a

Sunday, November 19, 2017

KO KASAN ILLAR APPS NA FACEBOOK KUWA?

Sanin kowa ne a lokutan da suka gabata, akan yi facebook ne ta hanyar opera, UC browser ko
kuma sauran browsers din kan waya. Ba da jimawa ba Facebook suka fara yin application na su
na kansu wanda za’a yi amfani da shi wajen yin facebook din. Lokacin da wannan application na
facebook ya fito, sun kashe makudan kudi wajen tallata wannan application a wajen mutane. Har
ta kai ma yanzu ko da wace irin browser ka shiga Facebook zaka ga suna yi maka tallar cewa
kayi installing na application dinsu a maimakon yin Facebook din a cikin browser din ka.
Shin kuna tunanin cewa haka nan kawai Facebook ke kokarin tabbatar da cewa kowa ya mallaka
tare da yin amfani da wannan application na su? Amsar wannan tambayar itace A’A! Facebook
sun yi haka ne domin su cimma wata manufa ta su.
Mun yi bincike mun gano wadannan boyayyun manufofin tare kuma da dalilan da zasu sanya ku
koma yin Facebook ta hanyar browser dinku ku kyale Facebook app. Wadannan dalilan su ne
kamar haka:
1. Taka dokar ‘Yancin dai-daito tsakanin Shafukan Internet
Akwai wani abu da ake kira da “Internet Neutrality”, wato baiwa ko wane shafin internet karfi
iri daya ta yanda babu wani shafi da zaya fi wani karfi ko kuma sauri. Akwai wasu kamfanoni
manya-manya kamar su Google da shi facebook din, da suke bukatar su zama sune ke control na
yanda za’a iya shiga sauran kananun shafukan Internet. Wannan doka ta zama kamar cikas ce ga
su wadannan manyan shafukan. Tunda Facebook sun fahimci cewa ba zasu iya yin hakan ta
hanyar browsers ko kuma network ba, sai suka bullo da shawarar kir-kirar application nasu na
kansu, ta yanda zasu iya control din shafukan da mutane zasu iya ziyarta. Ga dukkan wanda ke
amfani da application na facebook ya san cewa, yana da matukar wuya ka iya ziyartar wani shafi
kai tsaye daga cikin application din. Kamar yanda abin yake a whatsapp da sauran apps, idan aka
turo da wani link, in har kana so ka ziyarci wannan link din, to da zarar ka taba shi zaka ga
application din ya tambayeka cewa “da wace browser kake son bude wannan link din”. To abin da
Facebook suka yi shine, sai suka kir-kiri wata browser ta karyar daga cikin application dinsu, ta
yanda ko da ka taba link (misali idan kana son karan labaran wata jarida da suka yi posting), to
ba zata baka damar ziyartar wannan shafin ba, sai dai kawai ka ga yana ta loading kamar zaya
bude, amma kuma baya budewa.
2. Saurin Zuke/kwashe Data
Facebook sun fahimci cewa mafi yawan browsers din da ake amfani da su a wayoyi suna da
iyaka akan abin da zasu iya nunawa a ko wane page da suka bude. Su kuma Facebook suna
bukatar tabbatar da cewa duk wani page da ka bude na su, to sai sun samu wasu kudi da kai ta
hanyar nuna wasu tallace-tallace. Har wa yau da suka ga babu yanda zasu iya yi su nuna muku
abubuwan da suke bukata ta hanyar browser, sai suka bullo da wannan dubara ta application na
su, domin samun damar nuna duk wani abin da suke bukatar nunawa. Baya ga tallace-tallace na
rubutu da hotuna, sukan nuna tallace-tallace da ke dauke da videos. Wannan abubuwa da suke
nunawa a cikin wannan app na su, shi ke sanyawa a cikin dan lokaci sai kaji mutum yace wai
sub dinshi ko kuma data din shi ta kare. Ba wai datar ce ke rage karko ba, a’a abubuwan da ake
nunawa ne a cikin application din suke da yawa shi ya sanya ake saurin kwashe data din.
3. Cunkushe Memorin Waya
Tun da Facebook sun fahimci cewa ba lallai ba ne a ko da yaushe ka shiga wannan application
nasu ba. Wata rana mutum zaya iya shiga facebook din ta hanyar browser din shi, ya kyale app
din. Wannan ya sanya suka yi programming din application dins ta yanda duk wani abu da ya
shigo to ba zaya fita ba sai dai kawai ya cike ma mutum memory ta yanda sauran applications ba
zasu samu wadataccen space ba, sai bar yin sauri kamar yanda ya kamata. Idan har hakan ta
faru, sun tabbatar da cewa zaka koma ma application dinsu saboda zaka ga cewa kamar shi ne
yafi sauri. Sanin kowa ne a lokacin da kayi downloading na application din, zaka ga baya da
nauyi. Amma bayan kayi installing dinshi, ka shiga cikin “Application Manager” (idan da
android kake amfani), zaka ga ya zama mai wani irin nauyi (sama da 100MB).
4. Tilastawa mutane amfani da Facebook Messenger
A binciken da Facebook suka yi, sun gano cewa ta hanyar instant messenger (wato app da ake
chatting da shi kai tsaye) mutane sun fi bata lokacinsu. Sai suka fito da dubarar hana yin
message kai tsaye daga cikin Facebook app har sai kayi installing din Messenger, wanda hakan
shima zaya sanya su kara samun wani control din a kan wayarka da kuma ma kai kanka.
Wadannan ne kadan ne daga cikin wadannan boyayyun manufofi na Facebook wanda ba kowa ne
ya gano su ba. Idan kana amfani da wannan application din na Facebook, to ka jaraba
Unistalling din shi, tare da yin facebook din kai tsaye ta hanyar Opera ko kuma wata
browser, wannan shine zaya tabbatar maka da cewa dukkan wadannan abubuwan da muka fada
gaskiya ne. Baya ga haka kuma, zaku kara tattalin data dinku, ta yanda zaku rika yin abubuwa da
yawa da ita ba tare da tayi saurin karewa ba.

KASAN TARIHIN KASAR NIGER KUWA?

Mikasani Game Da Niger???
Niger kasace mai kabilu Yan kadan
Mai jahohi 7 gami da Capitale dinsu 8
Niger tanada zafin rana kware
Niger Sunada karancin ruwan sama
Niger tashahara da Zaman Lafiya
Niger tashahar da gaskiya wajan
talakawa
Niger 99% musulmane
Niger tashahar da dabbobi
Niger tashahara da kiyo
Niger tashahara da noms
Niger mutanan cikinta basukai Milyon
20 bâ
Niger sunada Arzikin Kalkashin kasa
Kamar man petur da Zinariya da
Uranium da gawayi da tagulla
Amma dayawa daga yan kasar
Abincinci namasu wuya
Niger tashahara wajan yima za6a66an
shugaba juyin mulki
Zamucigaba Acikin shirinmu na
mikasani game da niger
Insha Allah.

SAKON GARABASA FIYANYAN HALITTA S.A.W

Dr Isah Aliyu Pantami's*
*Da'awa page:*
*" GARABASA ME TARIN YAWA DAGA BAKIN FIYAYYEN HALITTA.*
*Duk wanda ya manta da Allah to shima Allah zai manta da shi.**
*Manzon Allah S. A. W. Yace duk wanda ka ganshi yana zaune yana jiran SALLAH ta zo ta sameshi a
masallaci ko a gidanta , ta/yayi Alwala yana jiran lokachin SALLAH yayi don yayi sallar. Annabi yace irin*
*wadannan mutanen koda ka gansu a waje suna aikata wani aiki na laifi to kayi musu uzuri, maganar imani
karka hada kanka da su domin sun fika imani, duba cikin kitabul ta'allimun.*
*Duk wanda ya ce subhanallahy wal hamdu LILLAHY WA laa ilaaha illallahu wallahu akbar*
*sau dari da safe dari da yamma*
*1. za a gafarta masa zunubai guda dari*
*2. za a bashi ladan yayi sadaqah da jajayen rakumai guda dari,*
*3.kuma za a rubuta cewa kowanne rakumi yana dauke da kayan abinci a kansa,*
*4.sannan za a rubuta masa ya "yanta bayi guda dari.*
*5.kuma darajar bayin ta kai darajar yayan annabi sulayman A. S.*
_*ALLAHU TA'ALA* akbar kabeeran! Allah bai sanya wannan *GARABASA* a ko ina ba sai a addinin
musulunchi addini cikakke._
_Yi kokari ka turama koda group ukku kokuma mutum goma don ALLAH zaka sami lada me Tarin yawa._
_Allah ina rokonka duk wanda ya tura wannan sako wa yan uwa musulmai Allah ka rufa masa asiri a filin
kiyamah kuma ka yaye masa bakin cikin duniya da na lahira._

Friday, November 17, 2017

SAFIN TUMBLR

https://superblyfullfury-a3d95aca.tumblr.com/post/167582694273/kudanna-06-akan-wayoyinku-babu-ruwanku-da

HANYAR NEMU WAYAR DA TABACE CIKIN SAUKI

Kudanna *#06# akan wayoyinku
babu ruwanku da danna kira da zaran
kun danna lambobin nan zakuga
wasu lambobi sun bayyana akan
wayar taku. Lambobin adadinsu guda
15 sune ake kira da IMEI NUMBER. Da wannan lambar za'ayi amfani a iya
gano inda kake matukar kana tare da
wayan kokuma agano inda wayan
taka take yayin da take hannun wani,
kuma koda ancire layuka da suke kan
wayan za'a iya ganowa ta hanyar amfani da wadannan lambobin.
Yana da kyau kowa yasan lambar IMEI
na wayar dake hannunsa domin tsaro
ba dan tsoro ba, musamman idan
kasan wayan hannunka baka saya da
kwalinta ba. Hakan zai baku daman bada kariya na musamman ga
wayoyin tarho dake hannayenku.
Ku bada lambar IMEI naku ga iyalai da
abokanku domin idan kuka bata ko
ankira baku dauka ba kokuma
wayarku ta shiga hannun bata gari zai zamo hanya mafi sauki wajan samar
da da inda kake ko wayan take. Allah
yatsare.
Zakuji kwana 2 inata maganan wayar
salula da irin hanyoyin bata kariya ko?
Himmmm nasha walaha batar wayoyi ne a baya. Dan Allah a aika ga sauran
'yan'uwa da abokan arziki.
Kuyi sharing Domin wadanda basa
tare damu anan suma su gani su
Amfana

ANFANIN AYABA (BANANE)

AMFANIN AYABA A jikin Dan ADAm 1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake s...