Total Pageviews

Sunday, November 19, 2017

KO KASAN ILLAR APPS NA FACEBOOK KUWA?

Sanin kowa ne a lokutan da suka gabata, akan yi facebook ne ta hanyar opera, UC browser ko
kuma sauran browsers din kan waya. Ba da jimawa ba Facebook suka fara yin application na su
na kansu wanda za’a yi amfani da shi wajen yin facebook din. Lokacin da wannan application na
facebook ya fito, sun kashe makudan kudi wajen tallata wannan application a wajen mutane. Har
ta kai ma yanzu ko da wace irin browser ka shiga Facebook zaka ga suna yi maka tallar cewa
kayi installing na application dinsu a maimakon yin Facebook din a cikin browser din ka.
Shin kuna tunanin cewa haka nan kawai Facebook ke kokarin tabbatar da cewa kowa ya mallaka
tare da yin amfani da wannan application na su? Amsar wannan tambayar itace A’A! Facebook
sun yi haka ne domin su cimma wata manufa ta su.
Mun yi bincike mun gano wadannan boyayyun manufofin tare kuma da dalilan da zasu sanya ku
koma yin Facebook ta hanyar browser dinku ku kyale Facebook app. Wadannan dalilan su ne
kamar haka:
1. Taka dokar ‘Yancin dai-daito tsakanin Shafukan Internet
Akwai wani abu da ake kira da “Internet Neutrality”, wato baiwa ko wane shafin internet karfi
iri daya ta yanda babu wani shafi da zaya fi wani karfi ko kuma sauri. Akwai wasu kamfanoni
manya-manya kamar su Google da shi facebook din, da suke bukatar su zama sune ke control na
yanda za’a iya shiga sauran kananun shafukan Internet. Wannan doka ta zama kamar cikas ce ga
su wadannan manyan shafukan. Tunda Facebook sun fahimci cewa ba zasu iya yin hakan ta
hanyar browsers ko kuma network ba, sai suka bullo da shawarar kir-kirar application nasu na
kansu, ta yanda zasu iya control din shafukan da mutane zasu iya ziyarta. Ga dukkan wanda ke
amfani da application na facebook ya san cewa, yana da matukar wuya ka iya ziyartar wani shafi
kai tsaye daga cikin application din. Kamar yanda abin yake a whatsapp da sauran apps, idan aka
turo da wani link, in har kana so ka ziyarci wannan link din, to da zarar ka taba shi zaka ga
application din ya tambayeka cewa “da wace browser kake son bude wannan link din”. To abin da
Facebook suka yi shine, sai suka kir-kiri wata browser ta karyar daga cikin application dinsu, ta
yanda ko da ka taba link (misali idan kana son karan labaran wata jarida da suka yi posting), to
ba zata baka damar ziyartar wannan shafin ba, sai dai kawai ka ga yana ta loading kamar zaya
bude, amma kuma baya budewa.
2. Saurin Zuke/kwashe Data
Facebook sun fahimci cewa mafi yawan browsers din da ake amfani da su a wayoyi suna da
iyaka akan abin da zasu iya nunawa a ko wane page da suka bude. Su kuma Facebook suna
bukatar tabbatar da cewa duk wani page da ka bude na su, to sai sun samu wasu kudi da kai ta
hanyar nuna wasu tallace-tallace. Har wa yau da suka ga babu yanda zasu iya yi su nuna muku
abubuwan da suke bukata ta hanyar browser, sai suka bullo da wannan dubara ta application na
su, domin samun damar nuna duk wani abin da suke bukatar nunawa. Baya ga tallace-tallace na
rubutu da hotuna, sukan nuna tallace-tallace da ke dauke da videos. Wannan abubuwa da suke
nunawa a cikin wannan app na su, shi ke sanyawa a cikin dan lokaci sai kaji mutum yace wai
sub dinshi ko kuma data din shi ta kare. Ba wai datar ce ke rage karko ba, a’a abubuwan da ake
nunawa ne a cikin application din suke da yawa shi ya sanya ake saurin kwashe data din.
3. Cunkushe Memorin Waya
Tun da Facebook sun fahimci cewa ba lallai ba ne a ko da yaushe ka shiga wannan application
nasu ba. Wata rana mutum zaya iya shiga facebook din ta hanyar browser din shi, ya kyale app
din. Wannan ya sanya suka yi programming din application dins ta yanda duk wani abu da ya
shigo to ba zaya fita ba sai dai kawai ya cike ma mutum memory ta yanda sauran applications ba
zasu samu wadataccen space ba, sai bar yin sauri kamar yanda ya kamata. Idan har hakan ta
faru, sun tabbatar da cewa zaka koma ma application dinsu saboda zaka ga cewa kamar shi ne
yafi sauri. Sanin kowa ne a lokacin da kayi downloading na application din, zaka ga baya da
nauyi. Amma bayan kayi installing dinshi, ka shiga cikin “Application Manager” (idan da
android kake amfani), zaka ga ya zama mai wani irin nauyi (sama da 100MB).
4. Tilastawa mutane amfani da Facebook Messenger
A binciken da Facebook suka yi, sun gano cewa ta hanyar instant messenger (wato app da ake
chatting da shi kai tsaye) mutane sun fi bata lokacinsu. Sai suka fito da dubarar hana yin
message kai tsaye daga cikin Facebook app har sai kayi installing din Messenger, wanda hakan
shima zaya sanya su kara samun wani control din a kan wayarka da kuma ma kai kanka.
Wadannan ne kadan ne daga cikin wadannan boyayyun manufofi na Facebook wanda ba kowa ne
ya gano su ba. Idan kana amfani da wannan application din na Facebook, to ka jaraba
Unistalling din shi, tare da yin facebook din kai tsaye ta hanyar Opera ko kuma wata
browser, wannan shine zaya tabbatar maka da cewa dukkan wadannan abubuwan da muka fada
gaskiya ne. Baya ga haka kuma, zaku kara tattalin data dinku, ta yanda zaku rika yin abubuwa da
yawa da ita ba tare da tayi saurin karewa ba.

No comments:

Post a Comment

ANFANIN AYABA (BANANE)

AMFANIN AYABA A jikin Dan ADAm 1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake s...