Total Pageviews

Tuesday, April 4, 2017

Kaso mutum amma kuma kayi hassada

KASO MUTUM AMMA KUMA KAYI HANKALI DA MUTUM...
.
Saboda shi 'dan-Adam da kuke ji da gani, babu mai iya masa, sai ALLAH..
.
Mutum ne zai yi maka fatan alkhairi, amma da zarar alkhairin yazo shine na farko da zai fara nuna hassadarsa gareka...
.
Mutum ne zaka yi masa alkhairi sama da sau 100, amma ranar da kai Kkskure guda 1, to fa dukkan alkhairan nan sun rushe....
.
Mutum ne yake rububin ka idan yaga wata dama ta sameka, amma da zaran wannan damar ta ku6uce maka, shikenan ba zaka sake ganinshi a inuwarka ba...
.
Mutum ne zaka yi masa alkhairi, daga karshe ya rasa abinda zai saka maka dashi; sai dai yayi maka sharri don nuna nasa salon adalcin....
.
Mutum ne yana hangen wata matsala na iya samunka, amma ba zai sanar maka da ita ba, sai bayan ta faru ko kuma a qurarren lokaci, ta yanda baka da wani matakin dauka illa ka auka cikinta....
.
Mutum ne za ka rikeshi amana, amma shi yaci amanar ka ba tare da ya ji komai a ransa ba....
.
Mutum ne idan ya ga samun duniya a gareka, zai zo ya raba ka da mutanenka na asali da amana, wadanda suka san mutuncinka, halan ma kuka sha wahalar rayuwa tare dasu a baya, amma da ta gushe maka shi kuma sai ya qara gaba ya gudu ya barka...
.
YA ALLAH muna roqonka kai cire mana mugunta, kyashi, da hassada a cikin zuqatanmu; Ka hada mu da mutane masu kaunar mu na gaskiya, kuma tsakani da ALLAH ba wai saboda wani abu na duniya da ka mallaka mana ba...

No comments:

Post a Comment

ANFANIN AYABA (BANANE)

AMFANIN AYABA A jikin Dan ADAm 1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake s...