AMFANIN AYABA A jikin Dan ADAm
1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake samu a cikin Carbohydrates, ba shakka yakan taimaka wajen rage qiba, ta yadda jikkuna za su fara diban wannan starch din a hankali, a sannan mutum zai riqa jin cewa ya qoshi, sai ya rage gabzar abincin.
2) Ayaba takan sassautar da hauhawar jini, don tana da Potassium, shi kuwa yana da mahimmanci wajen wannan aikin.
3) Zai yi kyau mutum ya sanya Ayaba a matsayin dan abin da zai riqa jefawa a baki lokaci zuwa lokaci kafin cin abinci, ya fi mutum ya ci abin da zai qara masa qiba, idan ya ji wata ‘yar kasala sai ya janyo guda ya kada ta a baki ya laqaqe ta, ta ma fi wasu juice din da suke dauke da Caffeine, masamman yadda ba ta da sukari sosai don dacewa da ci lokaci-lokaci, kamar in mutum yana wajen aiki, ko tarurrukan da kan dauki dogon lokaci, ko ma kallon talabijin.
4) Ayaba takan kusan zama wajibi ko don lafiyar hanji, Ayaba qwara daya tal za ta iya yi wa matum maganin basir, don tana da wani nau’in Fibres na masamman wanda yake taimaka wa hanji wurin aikinsa, wannan magani halittacce ya fi qara lafiya sama da magungunan Bature, masamman wadan da suke da side effect.
5) Banda wannan kuma Ayaba takan sanya kwanciyar hankali da dadin rai, domin tana da sinadarin Tryptophane wanda daya ne daga cikin sinadarorin da suke natsar da mutum da ba shi kwanciyar hankali na haqiqa, ta daidaita tsarin Protein a jiki, don ba wa mutum cikakkiyar sakewa.
6) In da a ce mutum zai riqa cin Ayaba sau uku a rana, wato wajen kari da wurin kalacin rana ko na maraice to Potassium din dake cikinta zai qarfafa qwaqwalwarsa, don dalibai kuwa yakan fi amfani don yakan qara musu concentration sosai a lokacin daukar darasi.
7) Game da mata masu ciki kuwa Ayabar takan taimaka don tana da fa’ida ba qarama ba ga mai juna biyu, masamman lokacin da take jin laulayi ko tashin zuciya wanda yake yawan faruwa in cikin yana qarami, sannan Ayabar za ta iya taimaka musu wajen ganin Glucose dake cikin jininsu bai nemi qaruwa ba, takan kuma lura da yanayin zafin jiki.
8) Sai kuma zancen cizon sauro, wani in sauro ya cije shi sai ka ga wurin ya yi hulu-hulu, to a irin wannan yanayin za a iya bare Ayaba a sanya bawon a wurin, don yakan magance qaiqayin da wurin yakan yi, shi ma wannan ya fi aminci sama da magungunan da mutum zai yi tashafawa.
9) Ayaba takan taimaka kuma wajen magance Ulcer, ko kuma riga-kafin hakan, domin takan taimaka wajen qanqanta Acid din da abinci yakan bari a tumbi, tawajen daidai acids din narka abincin, da wannan sai ka ga ta yi maganin matsalolin tumbi da dama.
10) Ayaba tana da Iron sosan gaske ga wadan da suke da cutar fatarar jini ko Anaemia, don Iron din kan taimaka masamman ga qwayoyin jan jini wanda yake kula da dauko Oxygen, ya kuma tabbatar da cewa ruwan jiki wato white blood ya ba da gudummuwarsa wajen magance raunuka.
11) Wani abin mamaki Ayaba hatta a gona bawonta yana da amfani, don kuwa takan zama taki idan aka kai ta can, kenan a maimakon a riqa zubarwa gwara a kai shi can inda za a yi aiki da shi don abincin da za mu ci.
12) Ayaba takan taimaka sosai wajen kiyaye lafiyar qoda, ta yadda take qanqanta tura Calcium zuwa fitsari, da qaranta yuwuwar kamuwa da tsakuwar qoda, kamar yadda bincike ya gano cewa cin Ayaba yakan rage hatsarin kamuwa da kansar qoda, ta yadda aka sami mata wadan da suke cin Ayaba sau 4-6 a sati yadda suka nesanta da kamuwa da kansar qoda sama da wadan da ba sa ci, ban da wannan ma sinadarori masu dama da suke cikin Ayaba sun sanya tana iya kawar da matsalar Ulcer kai tsaye.
Galibin Ayaba har da karkasuwar nau’o’inta duk tana dauke da sinadarori kala daban-daban, akwai ma doguwar Ayaba wace yawancinta Inyamurai muke ganin suna sayar da ita, ba a iya cinta sai an soya, ko kuma a gasa ta a wuta, mukan ga ana sanya ta ne a abinci kamar shinkafa, sai a yanyanka ta a dora ta a sama, sunanta Plantain, sukan kira ta da Larabci “Mauzul Janna” ita wannan Ayaba tana da starch sosan gaske, kuma ba ta da sukari mai dama, ita ma tana da tasiri wajen kawar da maiqo a cikin jini, a taqaice dai ita ma ayaba ce.
Total Pageviews
Saturday, December 16, 2017
ANFANIN AYABA (BANANE)
APPLICATION NA DANDALIN DAMAGARAWA
Wednesday, December 13, 2017
NASHIHOHI35 DAGA BAKIN MALAM AMINU DAURAWA
______________________________________
1- ka fara yininka da sallar asubahi da azkar domin samun rabo da tsira.
2- ka zarce da istgfari har sai shaidan ya debe
tsammanin samun rabo a jikinka.
3-kar ka daina addu'a dumin itace igiyar tsira
4-ka tuna cewa mala'iku suna rubuta maganganunka.
5-kyawun yatsu shine ka rika qidaya TASBIH dasu.
6- idan ka shiga damuwa da qunci kace" la ila ha illallah".
7- ka sayi addu'ar talakawa da soyayyan marayu da kudadenka.
8-doguwar sujada 1 wanda aka yita saboda tsoron ALLAH yafi maka bene da aka gina na zinari.
9- ka tauna magana kafin kafadeta domin tana iya zama ajalinka.
10- ka guji addu'ar wanda aka zalunta da hawayen wanda aka hana.
11- kafin ka karanta jaridu da mujallu mai zai hana.kafara karanta alqur'ani.
12- ka zama dalilin gyaruwan iyalanka.
13- ka tilastawa ranka wurin bin dokokin Allah ,
domin ita rai tana umarni ne da sabon Allah.
14- kafin tsufar iyayanka ka daure ka samu yardarsu.
15-tsoffin tufafinka sababbi ne a wurin talakawa.
16- kar kayi fushi , domin rayuwa kadan ce ba kamar yadda kake tsammani ba.
17- tare dakai akwai wanda yafi kowa qarfi yafi kowa wadata, shine Allah.
18- kar ka rufe qofar tuba saboda sabon Allah.
19- sallah itace mafi alkhairin abun da zata taimakeka akan musibu da wahalhalu.
20- ka nisanci munanan zato, zaka huta kuma zaka hutar.
21- dalilin kowane damuwa juyawa Allah bayane, ka juyo zuwa gareshi mana.
22-kayi sallah irin wacce kakeso a shigar dakai qabari tare da ita.
23- idan kaji wanda yake gulma , kace dashi: yaji tsoron Allah.
24-ka dawwamar da kanka wurin karanta suratul MULK domin tana tseratarwa.
25- wanda aka hana( yayi hasara) shine wanda aka hanawa sallar dake cike da tsoron Allah , da idon dake zubar da hawaye.
26- kar ka cutar da bayin Allah nagari wadanda suka shagaltu da bautar Allah.
27- ka sanya soyayyar ka duka zuwa ga Allah da manzonsa.
28- ka yafewa wanda yayi gulmarka, domin ya baka kyautar kyakyawan aikinsa ne.
29- Sallah da ambaton Allah da karatun alqur'ani alqawurane masu nauyi akan qirjinka.
30- duk wanda ya tuna da zafin wuta zai iya hakuri akan sabon Allah .
31- indai ana dare gari yana wayewa, to watarana sai labari tsanani zai zama sauqi.
32- ka nisanci ANCE-KACE ( jita-jita) domin kai game da ayyuka kamar dutsene.
33- kayi sallah da tsoron Allah , domin duk abun da zakayi bayan sallar bai kai sallah ba.
34- ka sanya alqur'ani daf dakai , domin karanta aya daya acikinsa yafimaka duniya da abun dake cikinta.
35- rayuwa akwai dadi, mafi dadin rayuwa shine kaganka da iimaninka.
________________________________
ALLAH Yasa Mudace!
_________________________
Saturday, December 9, 2017
HANYAR DA ZAKABI DOMIN KARE KANKA DAGA KAMUWA DA ZAJJABIN CHIZON SABRO
Shimfida
Assalamu'alaikum jama'a barkan Ku da kasancewa da shafin Lafiyata a wannan lokaci
A yau ne wannan shafi mai albarka ya ke kawo muku rubutu akan cutar zazzabin cizon sauro,,wato a turance Malaria, alamomin ta da yadda za a kare kai daga kamuwa da wannan cuta.
To da farko dai kaman yadda kusan kowa yana jin ko ya taba jin an anbata sunan "Malaria" wato zazzabin cizon sauro. Wannan cuta na kashe dubban mutane a ko wacce shekara mussamman ma yankinmu na Africa wanda cutar tafi addaba. Haka ne ya sa wannan shafi ya daura damarar ilmintar da yan-uwa a takaice akan wannan cuta.
Mecece ita cutar ?
a takaice dai cutar zazzabin cizon sauro cuta ce da ke samuwa ta hanyar cizo da sauro ke yi wa dan-adam da ya ke dauka da wannan kwayar cuta ta malaria. Sauro ba a jikinsa cutar take ba, a'a sai ya ciji wani dan-adam dake dauke da wannan cuta a jikinsa kafinnan idan ya ciji wanda bai da kwayan cutan a jikin sa sai ya kamu. Dalili, ita wannan kwayan cuta ta malaria na zama cikin jini ne daga zaran sauron ya ciji mutum, kafin lokacin da za ta bayyyana alamominta a jikin dan-adam, shi ko sauro dama abincin sa jini ne. Wannan yasa cutar zazzabin cizon sauro ke yaduwa cikin al'umma cikin karamin lokaci idan har ba a dauka matakan kariya daga wannan cutar ba, wanda anan gaba za muyi dan bayanin yan wasu hanyoyi na samun kariya ga cutar.
Illar cutar
cutar na da illa kwarai da gaske, wanda ta kan kai ga:
• Hauka:
idan ba'a magance cutar da wuri ba har ta ci jikin mutum to takan taba kwa-kwalwa, daga nan sai ta juyar da kwakwalwar mutum har ya kai ga hauka ana cewa ai an masa sihiri ne, a'a ba wani sihiri malaria ce.
• Mutuwa:
cutar na saurin kisa idan akai mata sakaci ba'a samu anyi maganinta da wuri ba. domin tai karfi za tai ga kona jini da halaka sassan jiki masu muhimmanci kamar su hanta da sauransu.
Yanayin yaduwar cutar
cutar na yaduwa ta hanyar cizo na sauro kaman yadda muka dan yi tayani a baya.
Ita cutar ba kowanne sauro ke yada ta ba. iya macen sauron ce ke yada wannan cutar. ta kan dauko cutar daga cikin jinin mutum mai dauke da kwayar cutar, sa'annan tana cizon wanda bai da cutar, to ta yaba masa.
wannan cuta ta zazzabin cizon sauro ta kan shiga cikin jini ne yayin da sauro mai dauke da wannan cuta ya ciji mutum, daga nan za ta tafi zuwa hanta ta zauna har zuwa lokacin da za tai karfi ta fara bayyana alamomin ta a jikin mutum, kuma alamomin ta basa bayyana daga lokacin da sauron yai cizo ya saka kwayar cutar har sai ta kai tsawon kwana (10 -15) goma zuwa shabiyar kafin su fara bayyana.
Alamomin cutar
Alamomin cutar sun hada da:
• zazzabi
• amai
• ciwon gabobi
• ciwon kai
a wassu lokuta idan ta fara kamari takan haifar da alamomi kamar haka:
• shashshekewa (Convulsion)
• jiki zai ta kar-karwa
• ido zai yi yalo
• mutum zai na ganin abubuwa wanda shi mai lafiyan ba zai gani ba (Hallucination).
• Jan dogon numfashi (Deep breathing)
• mutum zai kode (alamun babu jini a jikin mutum)
Wadannan sune wassu daga cikin alamomi na cutar, da anga wani daga cikin alamomin to ai maza-maza a garzaya asibiti mafi kusa.
Hanyoyin da za a bi don kare kai daga kamuwa da wannan cuta
Akwai hanyoyi da za a bI don kare kai daga wannan cuta ta zazzabin cizon sauro.
Hanyoyin sune kamar haka:
• Tsaftace muhalli
Sauro na zama a wuri ko muhallinin da ke da Kazanta, don haka ne yasa duk wurin da ke da ciyawa ko kwata wanda ba a gyarawa sauro zai ta sintiri a wajen ko muhallin.
Idan aka ce tsaftar muhalli ba ana nufin cikin gida ba kawai a'a har da ma bandaki,cikin gidan Kansa,daki da bayan gida. idan akwai ciyawa a bayan gida a nome ta ko ai mata feshi. Idan kuma cikin gida ne mai ciyawa shima a gyara. Bandaki ma a rika wankeshi ana gyara shi. haka daki ma a rika tsaftace shi.
• Amfani da ragar sauro (Mosquitor net)
abu na biyu kuma mai muhimmanci wajen kare kai ga kamuwa da zazzabin cizon sauro shine amfani da raga ta maganin sauro (Mosquitor net).
Mosquitor net na dauke da sinadarin da ke
kashe sauro. Don hake ne nake shawartar wanda bashi da net da ya nemi net ya fara amfani da shi.
Tabbas idan aka dau wadannan matakai da muka zayyano to da yardar Allah an rabu da wannan cuta.
Rufewa
Daga karshe muna yi wa maziyarta shafinmu fatan alkaira,. Da fatan kuma zamu amfanu daga abinda muka karanta.
Bayan haka muna cewa maziyarta wannan shafi mai Albarka da su rika
Gayyato
abokanku da yan-uwa zuwa wannan shafi don suma su amfani.
Daga karshen-Karshe muna fada wa maziyarta shafin mu da su riika yin
Comment, Share da Tambayoyi.
ANFANIN AYABA (BANANE)
AMFANIN AYABA A jikin Dan ADAm 1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci don ta qunshi Starch wadda ake s...
-
Liste des Sultans du Damagaram (L'arbre généalogique) . Cette liste recense les Sultans de Zinder depuis 1731 : 1731 - 1746 : Malam Y...
-
Sanin kowa ne a lokutan da suka gabata, akan yi facebook ne ta hanyar opera, UC browser ko kuma sauran browsers din kan waya. Ba da jimawa ...
-
I'm using "DANDALIN DAMAGARAWA_7.4.apk", Download it from https://play.google.com/store/apps/details?id=dandalin.damagarawa2...